Iran: Majalisar dokoki ta tsige ministan tattalin arziki saboda hauhawar farashi

‘Yan majalisar dokokin kasar Iran sun kada kuri’ar tsige ministan harkokin tattalin arziki da kudi Abdonnasser Hemmati daga mukaminsa saboda matsalolin tattalin arziki da kuma

‘Yan majalisar dokokin kasar Iran sun kada kuri’ar tsige ministan harkokin tattalin arziki da kudi Abdonnasser Hemmati daga mukaminsa saboda matsalolin tattalin arziki da kuma faduwar darajar kudin kasar.

Hemmati ya rasa kuri’ar amincewa a zaman majalisar na wannan Lahadi inda ‘yan majalisa 182 daga cikin 273 suka kada kuri’ar tsige shi. ‘Yan majalisa tamanin da tara ne suka bukaci ya ci gaba da zama a kan mukaminsa.

A yayin Zaman ministan da kansa da shugaban kasar Masoud Pezeshkian sun halarci wurin, yayin da kuma ‘yan majalisar kan batun kudurin, amma dai kudirin ya wuce bayan samun rinjayen amincewa da shi.

Shugaba Pezeshkian ya kare Hemmati, tsohon gwamnan babban bankin kasar Iran, ya kuma ce kasar na cikin yakin tattalin arziki da makiya, kuma zargin juna ba zai magance wata matsala ba.

Ya jaddada cewa hadin kai da hadin gwiwa ne kadai mafita ga matsalolin da kasar ke fuskanta.

Hemmati ya kuma yi jawabi a zaman inda ya ce Iran na da karfin iko kuma za ta yi nasara a yakin tattalin arzikin makiya.

Wasu gungun ‘yan majalisa 91 ne suka fara shirin tsige Hemmati, saboda gazawarsa wajen daidaita kasuwanni da kuma dakile hauhawar farashin kayayyaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments