Sakatarin majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani ya soki kasashen yamma da kokarin tursasawa Iran kan shirinta na makamashin Nukliya da kuma makamanta masu linzami. Ya maimakon su dauki hanyar tattaunawa da diblomasiyya sai sukazami hanyar tursasawan da kuma nuna karfi.
Larijani ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da wata tashar talabijin ta cikin gida. Ya kuma kara da cewa, wani abin lura a bukatun wadan nan kasashe shi ne bukatar wai dole iran ta rage nisan makamanta masu linzami zuwa kilomita 500 kacal.
Larijina ya kara da cewa, kasashen yamma suna son su takaida hakkin kasar Iran ta kare kanta daga makiyanta, da sunan diblomasiyya. Sannan ya kara da cewa shirin makamai masu linzami na kasar Iran don kare kanta ne daga makiyanta, don haka duk wata bukata ta takaita su ba abin amincewa ne ga kasar Iran ba. Ya ce su suka fice daga yarjeniyar JCPOA sannan suka yi amfani da ita don zaluntar mu.
Dangane da kungiyar Hizbullah da kuma shugabanta shahida Nasurullah, ya ce alfakhari ne ga mutanen kasar Lebanon da kuma yankin da duniyar masu neman yenci. Hizbullah ta fi karfin kasar Lebanon, hark ace wace ta ke da asali a akida da kuma karbuwa a cikin kasar Lebanon.