Iran: Jami’an leken asirin IRGC sun kama wasu mutane 12 masu alaka da Isra’ila

Jami’an leken asiri na dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun tarwatsa wata hanyar sadarwa da ke da alaka da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila

Jami’an leken asiri na dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun tarwatsa wata hanyar sadarwa da ke da alaka da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke shirin aiwatar da wasu matakai na kawo cikas ga tsaron kasar Iran.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Lahadin, Rundunar IRGC ta sanar da cewa, an gano wasu mutane 12 na wata kungiyar da ke da alaka da Isra’ila tare da kame su a larduna shida na kasar, inda ta kara da cewa mutanen suna shirin kai hare-hare  a cikin kasar.

IRGC ta ci gaba da cewa Isra’ila ta sanya jerin wasu matakai na ta’addanci a cikin Iran a cikin ajandarta biyo bayan gazawar gwamnatin yahudawan da magoya bayanta na yammacin Turai da na Turai musamman Amurka wajen cimma ” munanan manufofinsu a yankin zirin Gaza da Lebanon.

“Don dakile wannan makarkashiyar, an gano wata hanyar sadarwa da ta kunshi wasu ‘yan amshin shata 12 na gwamnatin yahudawan,  wadanda suke da niyyar aiwatar da matakan kawo cikas ga ayyukan tsaro na kasa da cutar da  jama’a a larduna shida na kasar Iran, kuma an yi nasarar cafke su bayan gudanar da wasu ayyukan tsaro na sirri masu sarkakaiya, inji sanarwar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments