Iran : Jagora Ya Bayyana Ra’ayin Musulunci Kan Hakkokin Mata

Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncina Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya bayyana cewa Musulunci yana bai wa mata matsayi mai girma da daidaito tsakanin maza

Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncina Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya bayyana cewa Musulunci yana bai wa mata matsayi mai girma da daidaito tsakanin maza a rayuwar zamantakewa da siyasa, yayin da yake Allah wadai da “al’adun kasashen Yammacin duniya ” game da mata.

“Maganar Alkur’ani game da asali da halayen mata ita ce mafi girma,” in ji Ayatollah Khamenei a ranar Laraba, a wata ganawa da dubban mata daga yankuna daban-daban na kasar.  

A cikin jawabinsa, Jagoran ya yi nuni da halayen Fatemeh Zahra (amincin Allah ya tabbata a gare ta), ‘yar Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da zuriyarsa), yana yabon matan Iran saboda “suna samun wahayi daga irin wannan haske mai shiryarwa” da kuma ci gaba daidai da manufofinsu.

“A Musulunci, a cikin zamantakewa, kasuwanci, ayyukan siyasa, samun damar shiga mukamai na gwamnati, da sauran fannoni, mata suna da hakkoki iri daya da maza.

Daga cikin hakkokin mata, ya ambaci adalci a cikin dabi’un zamantakewa da iyali, tsaro, mutunci da girmamawa, da kuma daidaiton albashi ga daidaikun aiki, inshora ga mata masu aiki, da takamaiman tanadin hutu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted