Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya ba da gudummawar Riyal biliyan 40 ga wata kungiyar agaji da mai rajin ganin an sako fursunoni mabukata da aka samu da laifin aikata laifuffuka wandanda ba na son rai.
A duk shekara, a cikin watan Ramadan, wannan kungiya mai zaman kanta ta kan kaddamar da kiraye-kirayen bayar da tallafi don tara kudade da biyan Diya, ta yadda za a saki fursunonin da ake yanke musu hukunci bisa aikata laifukan da ba da gangan ba.
Taron dai ya hada jami’ai da masu ba da agaji a Tehran babban birnin kasar da kuma garuruwa daban-daban na kasar duk shekara.
Diya wani hakki ne da ake biya ga wanda aka kashe ga magadansa, ko aka yi wa rauni ko kuma ba daidai ba.
Ramadan, wata na tara na kalandar Musulunci, lokaci ne mai matukar muhimmanci ga musulmi, wanda yana da muhimmanci a kula da marasa galihu da kuma taimakon mabukata.
Hakan ne sanya irin wannan lokacin Jagoran kan yi afuwa, ko sassauci ga wadanda ake tsare da bisa aikata wani laifi.