Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Bakai, ya ce, Iran tana kokarin ganin cewa an gudanar da taron kungiyar kasashen musulmi domin tattauna batun barazanar tilasta mutanen Gaza yin hijira.
Haka nan kuma ya ce, wannan tunanin na korar falasdinawa daga Gaza, ba wani abu ba ne sai cigaba da kisan kiyashi, ta hanyar amfani da makamin siyasa.