Iran : ‘’Falasdinu Ta Al’ummar Falasdinu ce”_ Jagora

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa : Gabadayen Falastinu tun daga kogi har zuwa teku ta al’ummar

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa : Gabadayen Falastinu tun daga kogi har zuwa teku ta al’ummar Falasdinawa ce.

Jagoran ya jaddada goyon bayan Iran ne ga gwagwarmayar Falasdinawa kan kasarsu mai dimbin tarihi, tun daga kogin Jordan zuwa tekun Bahar Rum, kamar shafin offishin jagoran ya sanar.

Kallaman Jagoran na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da wata shawara mai cike da cece-kuce na kaurar da Falasdinawa daga zirin Gaza da kuma sanya Amurka ta karbe yankin da yaki ya lalata.

Ta hanyar yada wannan sako a cikin harsuna da dama, Iran ta nanata kudurinta na tabbatar da Falasdinu.

Shi dai shugaba Trump na Amurka ya tsaya kai da fata cewa “kowa na kaunar” shirinsa na Amurka ta kwace zirin Gaza.

Ya fadi hakan duk da irin watsi da suka da bayyana shirin nasa da al’ummar Falasdinawa da shugabannin Gabas ta Tsakiya da gwamnatocin kasashen duniya suka yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments