Iran : Dakatar da kisan kiyashi a Gaza, ‘’zakaran gwajin dafi ‘’ne ga  MDD”

Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta bayyana cewa “Kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a zirin Gaza ya zama

Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta bayyana cewa “Kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a zirin Gaza ya zama babban gwaji ga Majalisar Dinkin Duniya.

Idan muna son kungiya mai inganci kuma mai amfani, dole ne mambobinta su dauki matakin gaggawa tare da tsayin daka wajen dakatar da wannan zalunci da hukunta masu laifi.”

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya ce zasu hadu a birnin New York domin halartar taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya.

Wannan zaman dai na gudana ne a daidai lokacin da MDD ke bikin cika shekaru 80 da kafuwa, a daidai lokacin da muhimman ka’idojinta da manufofinta ke fuskantar barazanar da ba a taba ganin irinta ba da suka hada amfani da karfi, da rashin mutunta dokokin kasa da kasa, da rashin hukunta manyan laifuka na take hakkin bil’adama.

Kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a Gaza yana wakiltar mafi munin gwajin ingancin Majalisar Dinkin Duniya, inji kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted