Iran : daftarin kudurin da Canada ta gabatar, siyasa ce da kin jininmu

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa daftarin kudirin da kasar Canada ta gabatar yana cike da siyasa ne kawai hasali ma nuna kin jinin

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa daftarin kudirin da kasar Canada ta gabatar yana cike da siyasa ne kawai hasali ma nuna kin jinin Iran ne.   

Mataimakin Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya, game da daftarin kudurin da Canada ta gabatar, ya ce: “Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna adawarta ta musamman ga wannan daftarin, wanda aka yi shi bisa dalilai na siyasa, son rai, da kuma na neman haddasa barna.”

Gholamhossein Darzi, Jakadan Iran kuma Mataimakin Wakilin Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana a ranar Laraba, a lokacin zaman Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya na Uku kan kudurin kare hakkin dan adam na Canada kan Iran:

Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada cewa: “Mun yi watsi da abin da ke cikin wannan daftarin da kuma manufar da ke bayansa.

Mataimakin Wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya ce: Irin wadannan ayyuka suna raunana tattaunawa ta gaskiya, suna lalata aminci, wanda ya kamata ya jagoranci aikin Majalisar Dinkin Duniya a fannin hakkin dan adam.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted