Iran Da Turkmenistan Na fatan Karfafa Alakarsu

Kasashen Iran da kuma Turkmenistan sun kudiri anniyar karfafa alakar dake a tsakaninsu a bangarori daban-daban, in ji shugaba Masoud Pezeshkian. A wata ganawa da

Kasashen Iran da kuma Turkmenistan sun kudiri anniyar karfafa alakar dake a tsakaninsu a bangarori daban-daban, in ji shugaba Masoud Pezeshkian.

A wata ganawa da ya yi da ministan harkokin wajen Turkmenistan Avazgeldyevich Meredov a birnin Tehran, shugaban na Iran ya ce “An bayar da umarnin da suka wajaba ga hukumomin da abin ya shafa domin nazarin bangarorin da za su kara yin hadin gwiwa da gwamnatin Turkmenistan.”

Pezeshkian ya kuma yi ishara da wani taro da za a yi a birnin Teheran na tekun Kasbiya, inda ya kara da cewa Iran na kokarin fadada alaka a tsakanin kasashen Caspian bisa zaman lafiya, abokantaka, da kyakkyawar makwabtaka.

A yayin wannan ganawar, ministan harkokin waken Turkmenistan ya yaba da yarjejeniyoyin da aka kulla tsakanin kamfanonin Iran da Turkmen a fannonin sufuri da makamashi, ya kuma yi kira da a kara yin hadin gwiwa tsakanin Iran da Turkmenistan a dukkan bangarori.

Meredov ya kuma bayyana fatan cewa, gudanar da kwamitin hadin gwiwa kan harkokin tattalin arziki zai inganta dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu na da matukar muhimmanci ga gwamnatin kasar Turkmenistan, kuma muna son fadada huldar dake tsakanin kasashen biyu ta kowane fanni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments