Ministan al’adu na Iran Sayyid Abbas Salihi ne ya bayyana cewa Tehran da Riyadh suna kokarin bunkasa alakarsu ta fuskar al’adu.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr’ ya ambato ministan al’adun na Iran yana fadin haka a lokacin da ya gabatar da wani taron manema labaru a yau Lahadi.
Ministan al’adun na Iran din ya kuma kara da cewa; Tun bayan sake mayar da alakar jakadanci a tsakanin Iran da Saudiyya, an bude fagage da dama na bunkasa alaka. Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, a wannan lokacin Saudiyyar tana son ganin an bunkasa alaka a cikin fagage mabanbanta.
Bugu da kari ministan al’adun na Iran ya kuma bayyana cewa a halin yanzu an bude wata kafar alakar al’adun da kasar Masar, kuma wannan alakar za ta cigaba da tafiya akan hanyar da ta dace.