Kasashen Iran da Pakistan sun yi kira da a yi aiki tare da ya hada da kara dankon zumunci tsakanin yan majalisar domin tunkarar babban makiyinsu, kuma sun yi tir da matakin kai hare-hare da Isra’ila ke yi da kuma ta’adanci a yankin
A wani bayani da suka fitar a wata ganawa da suka yi a bayan taron yan majalisu da aka gudanara a yau laraba a birnin Islam Abad, mataimakin kakakin majalisar dokokin kasar iran Ali Nikbad da takwaransa na kasar Pakistan sardar ayaz sadiq sun jadda game da matsayin kasashen na irin gudunmawa da suke badawa a yankin dakuma lammuran da suka shafi kasashen musulmi
Nikbad ya bayyana gamsuwarsa game da sanin ya kamatan kasar Pakistan kuma yayi tir da hare haren ta’addanci da aka kai a baya bayan nan a birnin islam Abad, inda ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya shafa da ma alumma da kuma gwamnatin kasar Pakistan
Kana kuma ya jinjinawa kasar Pakistan game da goyon bayan da ta bawa Iran a lokacin yakin kwanaki 12 da Isra’ila a watan yuli , yace lokacin yayi da kasashen biyu dake makwabtaka da juna za su yi amfani da wannan damar wajen kara fadada alakar dake tsakaninsu