Iran Da Pakistan Sun Kulla Yarjeniyoyi Guda Biyar Kan Harkar Sadarwa Da Al’adu

Gidan talabijin da radiyo na kasar iran ya rattaba hannu kan yarjeniyoyi guda biyar da kafar sadarwa ta kasar Pakistan kan harkokin sadarwa da aladu

Gidan talabijin da radiyo na kasar iran ya rattaba hannu kan yarjeniyoyi guda biyar da kafar sadarwa ta kasar Pakistan kan harkokin sadarwa da aladu a wata ziyara da babbar tawagar kasar Iran ta kai birnin Islam abad na kasar Pakistan ,inda ya samu halartar ministan sadarwa da yada shirye shirye na kasar Attaullah Tarar.

Wadannan yarjiniyoyin ya nuna irin babban matakin da aka taka a bangaren diblomasiya na sadarwa tsakanin Tehran da kuma Islam Abad, wanda zai kara bunkasa alakar alaadu da sadarwa yadda zaa yi aiki tare a fadin kudancin Asiya.

Tawagar kasar iran da Ahmad Norouzi ya jagoranta shugaban bangaren gidajen radiyoyin  kasashen waje na gidan talabijin da redio na kasar iran su ne suka jagorancin sanya hannu kan dukkan yarjeniyoyi guda biyar da aka yi da suka shafi sadarwa da kuma aladu.

Ministan sadarwa na kasar Pakistan ya bayyana yarjeniyoyin a matsayin wata babbar alama ta kara karfafa alakar dake tsakaninsu a bangaren sadarwa yace zai taimaka sosai wajen tunkatar makircin kafafen sadarwa kasashen yamma da kuma samar da hadin kai tsakanin kasashen musulmi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted