Kasashen Iran da kuma Lebanon sun tattauna kan dangantakar dake a tsakaninsu dama halin da ake ciki a yankin.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da yammacin yau Asabar, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na Lebanon din Youssef Raji sun jaddada muhimmancin mutunta juna da hadin gwiwa.
Iran da Lebanon suna da dangantaka mai karfi da ta dogara da muradu guda, tare da ci gaba da tattaunawa don karfafa hadin gwiwa a cikin kalubalen da ake fama da shi a yankin.
Araghchi ya taya Youssef Raji murnar nadin da aka yi masa a matsayin sabon ministan harkokin wajen Lebanon, tare da yi masa fatan samun nasara a sabuwar gwamnatin Lebanon.
Ya jaddada mahimmancin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta bangarori daban-daban da suka hada da siyasa, tattalin arziki, kasuwanci, da al’adu.
Ministocin sun kuma tattauna kan bukatar tattaunawa don warware batutuwan da suka shafi jigilar fasinjoji tsakanin kasashen biyu.