Iran Da Iraki Sun Nuna Damuwa Kan Tashe-tahen Hankula A Siriya

Kasashen Iran da kuma Iraki sun nuna damuwa kan tashe tashen hankulan dake faruwa a Siriya. A wata sanarwa da ta fita ma’aikatar harkokin wajen

Kasashen Iran da kuma Iraki sun nuna damuwa kan tashe tashen hankulan dake faruwa a Siriya.

A wata sanarwa da ta fita ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana matukar damuwarta kan yadda tashe-tashen hankulan da ke yaduwa a fadin kasar ta Siriya, tana mai gargadin cewa, wannan yanayi mara kyau zai share fagen rashin zaman lafiya a yankin da kuma kara tunzura Isra’ila.

Kakakin ma’aikatar Esmail Baghai ya bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran na nuna damuwa kan rashin tsaro, tashe-tashen hankula, zubar da jini da cutar da al’ummar Siriya da basu ji basu gani ba.

Ita ma ma’aikatar harkokin wajen kasar Iraki ta bayyana matukar damuwarta kan halin da ake ciki a makwabciyarta Syria, tana mai jaddada cewa karuwar tashe-tashen hankula a kasar Larabawar ka iya yin tasiri sosai ga tsaro da zaman lafiyar yankin.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a Asabar din nan, ma’aikatar ta jaddada bukatar “kare fararen hula daga bala’in rikici.”tare da yin kira da a ba da fifiko wajen tattauna hanyoyin warware matsalar ta cikin lumana.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da wasu majiyoyi na cikin gida suka bayar da rahoton cewa, an gwabza kazamin fada tsakanin bangarorin da ke da alaka da gwamnatin Hayat Tahrir al-Sham (HTC) mai mulki da kuma ‘yan adawa masu biyayya ga tsohuwar gwamnatin, kusa da asibitin al-Watani da ke birnin As-Suwayda a kudu maso yammacin kasar Syria.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Syrian Observatory for Human Rights (SOHR) mai hedkwata a birnin Landan ta bayar da rahoto a jiya Juma’a cewa akalla mutane 237 ne aka kashe a yankin gabar tekun Syria tun bayan barkewar sabon tashin hankali a ranar Alhamis.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments