Jakadan kasar Iran a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Redha Najafi ya bayyana cewa Iran da hukumar nukiliya ta duniya sun koma teburin tattaunawa game da shirin nukiliya iran na zaman lafiya domin duba hanyoyin da zaa bi domin ci gaba da aiki tare,
Yace iran ta bar kofa a bude domin tabbatarwa da hukumar ta IAEA cewa lallai shirin nukiliyart na zaman lafiya ne zalla. kuma zaman ya kunshi wakilai daga nan Tehran da kuma wasu jami’ai daga maikatar harkokin waje da kuma hukumar kula da makamashin duniya ta iran.
Iran ta ce yanayin da ake ciki tun bayan harin da Amurka da Isra’la suka kai a tashoshinta na nukiliya dole ne ayi la’akari da alakar dake tsakaninta da hukumar a nan gaba,
Ganawar ta yau da hukumar IAEA ta gudana ne tsakanin ta da wakilai daga ma’aikatar harkokin waje da kuma ta hukumar nukiliya ta iran .