Kasashen Iran da Belarus, sun rattaba hannu kan wani daftari na bunkasa alaka ta haddin guiwar tsaro a tsakaninsu.
Ministan tsaron kasar Iran Aziz Nasirzadeh da takwaransa na kasar Belarus Viktor Khrenin ne suka rattaba hannu kan wata takarda kan fadada hadin gwiwar tsaron kasashen biyu.
An rattaba hannu kan takardar ne a wata ganawar da ministocin biyu suka yi a Minsk, babban birnin kasar Belarus, inda bangarorin biyu suka kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaro da kuma hanyoyin zurfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu da inganta hadin gwiwar soji.
A yayin ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan batutuwan da suka shafi tsaro tare da yin musayar ra’ayi kan hanyoyin zurfafa dangantakar dake tsakaninsu.
A yayin wannan taron, ministan tsaron kasar ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar tsaro, musamman ta hanyar yin amfani da karfin kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da kasancewar kasashen biyu a cikin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, wajen tinkarar barazanar bai daya.
Ya bayyana rattaba hannu kan wannan takarda a matsayin wani muhimmin mataki na karfafa huldar tsaro da tsaro tsakanin Tehran da Minsk.
A nasa bangaren, Janar Viktor Khrenin, ministan tsaron kasar Belarus, ya jaddada bukatar ci gaba da hadin gwiwar tsaro, domin tabbatar da tsaro mai dorewa.