Mataimakin shugaban kungiyar Iraniyawa masu bayar da kyautar gabban jikinsu ga mabukata, Umid Qabadi, ya bayyana cewa; A cikin shekaru 25 da su ka gabata, yadda ake kyautar gabban jiki domin yin dashe a duniya ya karu da kaso 70%, kuma Iran ce ta farko wajen yin dashen koda, har ma ana yi ma ta kirari da; Sarauniyar dashen koda.”
A yayin wani taro na girmama masu bayar da kyautar gabban jikin nasu domin yi dashe ga mabukata a gundunar Qazwin, mataimakin shugaban kungiyar Umid Qabadi ya ce; Iran ce ta farko a duniya wajen yin dashen gabobi ga marasa lafiya mabukata.
Qabadi ya yi ishara da wajabci ganin an bunkasa wannan al’ada ta bayar da gabobin jiki domin yin dashe saboda a ceto da rayukar mutane, yana mai kara da cewa; A gundumar Qazawin a shekarar da ta gabata, mutane 12 sun bayar da kyautar gabobin jikinsu ga mabukata. Amma a cikin watanni biyu na wannan shekarar kadai, an sami mutane bakwai da su ka bayar da kyautar gabobin jikin nasu ga mabukata.”
Har ila yau, mataimakin shugaban kungiyar masu bayar da gabobin jikin nasu ga mabukata ya ambaci cewa; An kafa wani tsari a Iran na yin jigila ta sama ta marasa lafiya da suke da bukatar a yi musu dashe, zuwa wasu gundumomi na kasar.
Qabadi ya ambaci cewa; A shekarar 1989 ne wanda ya assasa jamhuriyar musulunci ta Iran, Imam Khumaini ( QS) ya bayar da fatawar halarta bayar da gabobin jiki domin ceto da marasa lafiya mabukata, daga wadanda su ka rasu ta hanyar bugun kwakwalwa.” Qabani ya bayyana wanann fatawar a matsayin daya daga cikin muhimman ci gaban da juyin musulunci ya samar.