An bayyana cewa Iran ce kasar ta 10 a duniya wajen samar da wutar lantarki, da yawan megawati dubu 94 da 846.
Manajan da yake kula da tsara manyan ayyuka a ma’aikatar makamashi ta Iran, Behruz Muradi ya bayyana cewa, shekru 46 da su ka gabata, wato a lokacin juyin juya halin musulunci, yawan megawatin da Iran take samarwa ya yi kasa da wanda ake da shi a yanzu har sau hudu.
Manajan ya kuma kara da cewa wutar lantarki da ake da ita a Iran da karfin tsarin da take da shi, tana taka rawa mai muhimmanci wajen gina tattalin arzikin kasar. Haka nan kuma ya ce, da akwai kyakkyawan tsarin da ake da shi ya samar da cigaba a cikin bangarorin ruwan sha, da kuma noma da kiwo.
Behruz Muradi ya kuma ce, ci gaban da aka samu a fagen wutar lantarki a Iran yana daga cikin nasararon juyin juya halin musulunci.
Hanyoyin da Iran take samar da wutar lantarki, sun hada da madatsun ruwa, iska, hasken rana da kuma wasu sabbin hanyoyin na zamani.
Dangane da yawan garuruwan da suke da wutar lantarki a Iran, manaja Muradi ya ce, A halin yanzu da akwai kauyuka da sun kai 58,000, da 829 da suke da wutar lantarki.