Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya fadi cewa iran tana ci gaba da aiki da diplomasiya duk da cikas da Amurka take kawo wa a tattaunawar da ba ta kai tsaye ba, ganin cewa Amurka tana amfani da karfi wajen gudanar da harkokin duniya .
Yace idan bangaren Amurka ta nuna shirinta na yin tattaunawa bisa mutunta jina da kare munufofin kowa, to iran za ta iya duba lamarin, saboda bamu taba barin teburin tattaunawa ba , saboda it ace ingantacciyar hanya ta fuskantar alumma.
Dangane da Ziyarar da ya kai a bayan bayan nan a garin muscat da kuma tarurrukan da yayi, babban jami’in diplomasiyar iran yace babban abin takaici shi ne inda dokokin kasa da kasa da tsarin duniya suke kara yin tasiri ga yanayin Amurka na amfani da karfi a dangantakar kasa da kasa.
Daga karshe yace akwai bukatar gina tsaro a iyakokin kasashen yankin ba tare da tsoma bakin kasashen waje ma’abota girman kai ba, wanda wannan ne zai kara samar da yarda da zai sa akulla yarjejeniyar tsaro a yankin tekun fasha.