Kwamitin koli na tsaron kasa a cikin majalisar shawawar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; Saboda yadda hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa ( IAEA) take ci gaba da siyasarta na nuna wariya, ci gaba da aiki da ita ba shi da wani alfanu a wurin Iran.
Shugaban kwamitin tsaron kasar a majalisar shawarar musulunci ta Iran Ibrahim Azizi ya bayyana cewa; Karkataccen rahoton da hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa ya gabatar ne ya zama abinda HKI ta fake da shi wajen kawo wa Iran hari na ta’addanci.
Azizi ya kara da cewa; Iran ta sha nanata cewa, shirinta na Nukiliya na zaman lafiya ne, kuma yana gudana ne a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman Nukiliya.
Ibrahim Azizi ya kuma kara da cewa; A lokuta da dama Iran ta karbi bakuncin shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa Grossy, ya kuma ziyarci cibiyoyin makamashin Nukiliya; amma wannan hukumar ta daina aiki da ilimi da kwarewa ta koma abin wasa a hannun manyan kasashe.
Haka nan kuma ya ce; Saboda yadda hukumar ta koma aiki da siyasar nuna wa Iran wariya, ci gaba da yin aiki da ita ba shi da wani alfanu ga Iran.