Iran ba ta amince da Amurka ba, amma za ta gwada su (Araghchi)

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya ce Amurka na da masaniya kan irin karfin kare kai da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke da shi, yayin

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya ce Amurka na da masaniya kan irin karfin kare kai da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke da shi, yayin da ya ce kasar ta shirya tsaf domin kare kanta.

Ya kuma jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta yarda da Washington ba, amma duk da haka za ta gwada ta yayin tattaunawar da za a yi nan gaba a ranar Asabar mai zuwa,” in ji Abbas Araghchi yayin wani taron manema labara a Aljeriya.

Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta neman yaki, amma idan ya zama dole ta san yadda za ta kare kanta. »

“Muna shakkar aniyar Amurka kuma ba mu da tabbacin cewa suna da niyyar gudanar da tattaunawa ta gaske, amma za mu gwada su.”

Kalaman na baya-bayan nan sun shafi tattaunawar da ake sa ran za a fara tsakanin Araghchi da manzon Amurka na yankin Steve Witkoff a Muscat babban birnin kasar Omani ranar Asabar tare da ministan harkokin wajen Omani Badr bin Hamad Al Busaidi a matsayin mai shiga tsakani.

Haka nan kuma jami’in diflomasiyyar na Iran ya yi watsi da zargin kasashen yamma – karkashin jagorancin Washington – cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran na neman mallakar makamin nukiliya.

Ya ce zargin da ake yi wa Iran na neman mallakar makamin nukiliya, zargi ne mara tushe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments