Iran : Araghchi zai ziyarci Pakistan da Indiya

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi yana shirin kai ziyara a kasashen Pakistan da Indiya a wannan makon a wani bangare na tuntubar juna tsakanin

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi yana shirin kai ziyara a kasashen Pakistan da Indiya a wannan makon a wani bangare na tuntubar juna tsakanin Tehran da kasashen yankin.

Ministan harkokin wajen Iran din zai isa Pakistan a ranar Litinin 5 ga watan Mayu, domin tattaunawa da manyan jami’an kasar.

Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da sabbin ci gaban yanki da na kasa da kasa, in ji kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, kafin ya tabbatar da cewa Mr. Araghchi zai kai ziyarar aiki a Indiya nan gaba a cikin mako.

Ziyarar na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin Indiya da Pakistan, kasashe biyu masu makamin nukiliya.

Wannan tashin hankalin dai ya ta’azzara ne sakamakon harin  da aka kai a yankin Kashmir da ke karkashin ikon Indiya a ranar 22 ga watan Afrilu, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 26.

Indiya dai na zargin Pakistan da hannu a harin, zargin da Pakistan din ta musanta.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da firaministan Indiya Narendra Modi a ranar 26 ga watan Afrilu, shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da harin, yana mai jaddada bukatar hadin gwiwa da yaki da ta’addanci.

A wata tattaunawa ta daban ta wayar tarho da firaministan Pakistan Shehbaz Sharif a wannan rana, Mr. Pezeshkian ya bayyana matukar damuwarsa kan yadda ake kara samun takun saka tsakanin Indiya da Pakistan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments