An zartar da hukuncin kisa a kan daya daga cikin manyan ma’aikatan leken asiri a Iran da ke aiki da hukumar leken asiri ta gwamnatin Isra’ila, Mossad, kamar yadda ma’aikatar shari’a ta Iran ta tabbatar.
An zartar da hukuncin ne a kan Bahman Choubi-Asl a ranar Litinin bayan samunsa da laifin haɗa kai tare da hukumar leƙen asiri ta Isra’ila a fagen tattara bayanai.
Ya kasance kwararre kan harkokin bayanai wanda ya shigo cikin muhimman ayyukan sadarwa na kasar ta hanyar kasancewarsa a wani kamfani na ayyukan kimiyya da fasaha.
Saboda kwarewarsa ya kasance a matsayin manaja a cikin dukkanin ayyukan kamfanin kuma yana da damar samun mahimman bayanai na kasar.
A cewar rahotannin bangaren shari’a, jami’an Mossad sun fara gano Choubi-Asl a lokacin da yake halartar kwas na ƙwararru a wata ƙasa a yankin tekun Farisa. Wani jami’in Mossad, wanda ke aiki a karkashin sunan wani kamfani mai suna “ESMI,” daga baya ya tuntube shi.
Da farko an umurci wanda ake tuhuma da ya tafi Armenia, ko da yake daga baya aka canza wurin ganawarsu zuwa Indiya tare da ba da umarnin ya kawo kwamfutar tafi-da-gidanka da yake gudanar da ayyukansa.
A yayin wannan tafiya, jami’an Mossad wadanda suke a matsayin shugabannin wani kamfani sun biya dukkan kudaden balaguron, sun ba da lamuni na kudi, kuma sun sanya shi cikin azuzuwan horar da fasaha don haɓaka kara kwarewa a fagen aikinsa.
Hakan ya biyo bayan wani gagarumin shirin horo na musamman na kwanaki 45 a Ireland, inda wani mai magana da harshen Farisanci ya yi masa bayani kan muhimman abubuwan more rayuwa na Iran da ayyukan adana bayanai.