Iran: An Gudanar da Gagarumin Bukin Haihuwar Limami Na 12 A Masalacin Jamkaran A Birnin Qom

A daren Laraban da ta gabata ce aka gudanar da gagarumin bikin haihuwar limami na 12 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon

A daren Laraban da ta gabata ce aka gudanar da gagarumin bikin haihuwar limami na 12 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Allah (s) wato Mohammad dan Hassan Al-askari wanda aka fi saninsa da Imam Mahdi a birnin Qum na ilmi dake kudancin birnin Tehran a nan JMI.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa taron na qom shi ne mafi girma tun bayan nasaral Juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran shekaru 47 da suka gabata. Sannan taron na bana yana cewa ne a dai dai lokacinda jiragen yakin Amura suke kawanya da JMI da nufin tumbuketa.

Imam Mahdi(a) dai shi limami na 12 daga limamai masu tsarki wadanda manzon Allah (s) ya sanyasu a matsayin khalifofinsa a bayansa har duniya ta nade. Na farkosu Aliyu dan Abitalib (a) sannan yayansa daga diyar manzon Allah (s) Fatima (s) sai kuma yayan Hussain guda 9 na karshensu shi ne Imam Mahdi (a). Kuma shi ne wanda Allah yayi alkawalin ciki duniya da adalci bayan cikarta da zalunci a karshen duniya.

A cikin musulmi dai mabiya mazhabar Shia mai limamai 12 ne da wasu tsirarun musulmi ne  kawai suka yi Imani da haihuwarsa a ranar 15 ga watan Shaaban shekara ta 255 bayan hijira, wanda ya nuna a halin yanzu yana da shekaru kusan 1200 a duniya.

Da fatan Allah ya gaggauta bayyanarsa don kubutar da bil’adama daga musifun da suka fada ciki a hannun azzaluman shuwagabannin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted