Iran : An Binne Shahid Ra’isi A Mahaifarsa Mashhad

A Iran, an binne gawar shugaban kasar Shahid Ibrahim Ra’isi, a mahaifarsa birnin Mashhad.   Wannan dai na zuwa ne a yayin da aka shiga

A Iran, an binne gawar shugaban kasar Shahid Ibrahim Ra’isi, a mahaifarsa birnin Mashhad.  

Wannan dai na zuwa ne a yayin da aka shiga kwana na hudu na zaman makokin da aka ayyana a kasar bayan rasuwar shugaban kasar da wasu mukarabansa yayin wani hatsarin jirgin helikwabta ranar Lahadi data gabata.

Kafin nan miliyoyin mutane a lardin Khorasan Razavi sun hallara domin yin bankwana da gawarsa da wasu mukaranbansa biyu da suka yi shahada a hatsarin jirgin.

Maganin garin Mashhad ya bayyana cewa mutane sama da miliyan uku suka halarci jana’izar mirigayin shugaban kasar.

Kafin ya zama shugaban kasar Ibrahim Ra’isi, ya kasance mai kula da masallacin Mashhad birni na biyu mafi girma a Iran, sannan wurin da ya kunshi hubarren Imam Reza(AS) limamin shi’a na takwas da ke tsakiyar birnin Mashhad.

Jama’a sanye da bakaken kaya rike hotunan shugaban tare da karrabansa na zubar da hawaye na nuna bacin rai game da rashin shugaban kasar.

Tun da fari dai, gawawakin Shahid Raeisi da mukarrabansa sun samu kyakkyawar tarba a Birjand, babban birnin lardin Khorasan ta Kudu, inda aka zabe shi a matsayin wakilin lardin gabas a zaben majalisar kwararru ta Iran a watan Maris.

Jiya Laraba ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranci Sallar Jana’iza wa gawarwakin shahiddan a Tehran babban birnin kasar a daidai lokacin da miliyoyin jama’a suka taru don gudanar da jana’izar.

Gobe Juma’a ne ake kawo karshen zaman makokin kwanaki biyar da aka ayyana na juyayin rasuwar manyan jami’an.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments