Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya bayyana a fili cewa babban abin da yasa kasar Amurka take adawa da kasar iran shi ne batun kafa jamahuriyar musulunci da kuma kin amincewa da baba kerenta, ba wai batun shirin nukiliyar ta ba da take fakewa da shi
haka zalika ya kara da cewa yana da kyau ka tuna cewa mun shiga zagaye 3 na tattaunawa da bangaren kasar Amurka , amma dukkan tattaunawar guda 3 an kare ne da kaddamar da yaki akan mu .don haka bamu da aminci da duk wani mataki da Amurka za ta dauka
Araqci ya kara da cewa adaidai lokacin da iran take shirye ta karbi duk wani mataki na diflomasiya haka zalika jamhuriyar musulunci ta iran a shirye take ta mayar da martani kan duk wanda yayi kokarin kai mata hari ko kaddamar da yaki akanta.
Daga karshe yace a hukumance iran ta gabatar da bukatunta da zai kawo karshen yakin da ake ciki, shi ne Amurka ta yi aiki da yarjejeniyar da aka cimma ta Islamabad , da kuma fahimtar juna da aka samu game da mashigar Hurmuz ta yadda za’a bude shi bisa yarjejeniyar da aka cimma , da kuma ci gaba da tattaunawa kan sauran batutuwan.