Iran ta ce a shirye ta ke ta tattauna da don yin shawarwari da kasashen turan nan uku na gungun E3, amma ba cikin matsin lamba ba.
Ministan harkokin wajen kasar ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganwa da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA Rafael Grossi dake ziyara a birnin Tehran.
Grossi ya iso Tehran ne jiya don tattaunawa da manyan jami’an nukiliya da na siyasa na Iran.
A cikin sanarwar da suka fitar ta hadin gwiwa, Tehran da hukumar ta IAEA sun amince da cewa, kyakkyawar huldar da ke tsakanin kasashen biyu za ta iya ba da damar kulla yarjejeniyoyin da ke tsakanin bangarorin.
Har ila yau, sun amince da cewa, za a gudanar da mu’amalar da ke tsakanin kasashen biyu bisa tsarin hadin gwiwa, da kuma daidai da cancantar hukumar ta IAEA.
A wani lokaci yau Alhamis Grossi zai gana da Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) Mohammad Eslami, sannan kuma yana shirin ganawa da Shugaba Masoud Pezeshkian.
Grossi da Eslami za su halarci taron manema labarai na hadin gwiwa.