Iran A Shirye Take Ta Hada kai Da Pakistan Don Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci

Babban Hafsan Hafsoshin kasar Iran ya bukaci kasar Pakistan ta bada hadin kai da JMI don kawo karshen ayyukan ta’addanci a kan iyakokin kasashen biyu.

Babban Hafsan Hafsoshin kasar Iran ya bukaci kasar Pakistan ta bada hadin kai da JMI don kawo karshen ayyukan ta’addanci a kan iyakokin kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Manjo Janar Abdurrahim Musavi yana fadar haka a lokacinda yake zantawa ta wayar taro da tokwaransa na kasar Pakistan Fiel Mashal Asim Munir a yau Talata.

Musavi ya godewa kasar Pakistan da taimakawa kasar a yakin kwanaki 12 na watan yunin da ya gabata., sannan yayi nuni da bukatar kasashen biyu su hada kai don murkushe ayyukan ta’addanci a yankin Sisitan Balucistan na kasar Iran da kuma cibiyarsu dake cikin kasar Pakistan.

Ya ce akwai bukatar kasashen biyu su hada kai a wannan fagen bayan an dauki shekaru ana kashe Jami’an tsaron  kasar Iran saboda ayyukan ta’addancin wacce cibiyarta ke cikin kasar Afghanistan.

Ya ce a cikin yan shekarun ne ayyukan ta’addanci sun karu a cikin yankin Sistan Baluchistan inda suke kashe fararen hula da kuma jami’an tsaro.

A ranar Jumma’an da suka gabata kadai yan ta’adda sun kashe Jami’an tsaron JMI har guda 5.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted