Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa bukatun Amurka marar kan gado ne suka hana a kai ga cimma yarjejeniya a tattaunawar data gudana a birnin Islamabad na Pakistan.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya bayyana a wannan Lahadin cewa bangarorin sun cimma matsaya akan wasu batutuwa amma akwai bangarori biyu zuwa uku masu mahimmaci da ba’a kai ga warware su ba, wanda ya sanya daga karshe ba’a samu cimma wata yarjejeniya ba.
Ya kara da cewa tattaunawar ta zo ne bayan kwashe kwanaki 40 na yakin da aka kallafa wa Iran, kuma ana cikin yanayi na rashin rashin yarda akwai wahala dama a ce an cimma matsaya, musamman a zagayen farko.