A jiya juma’a ne dai firma ministan kasar Iraki Muhammad Shi’ya al-Sudani ya sanar da cewa sojojin kasar sun kashe babban dan ta’adda Abdullahi Makki wanda ake yi wa lakabi da Abu Hadiza.
Al-Sudani ya kara da cewa; Iraki taba cigaba da samun nasara akan ‘yan ta’adda, bayan da jami’an tsaro na kasa da kasa su ka yi nasarar kashe Abdullahi al-makki, wanda ya kasance a matsayin mataimakin shugaban abind ake kira da Daular Musulunci a Iraki da Syria.