Iragchi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Babban Sakataren MDD Antonio Guterres

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Argchi ya zanta ta wayar tarho da babban sakataren MDD Antonio Guterres inda ya fada masa inda aka kwana

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Argchi ya zanta ta wayar tarho da babban sakataren MDD Antonio Guterres inda ya fada masa inda aka kwana a tattaunawar da kasarsa take da Amurka ba kai tsaye ba.

Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto Arigchi yana fadawa babban sakatarin kan cewa akwai bukatar bangarorin biyu su yi gaske don cimma yarjeniya wacce kowa ya amince da ita.  Wannan tattaunawar tana da muhimmanci a wajen Iran don itace zata fauuace makomar shirin nukliyar kasar Iran. Da kuma takunkuman zaluncin da Amurka ta dorawa kasar.

Tattaunawar dai tana nuna irin yadda Iran ta fifita tattaunawa da kuma hanayr diblomasiyya kan shiga wasu rigingimu wadanda basa da amfani.

Aragchi ya fadawa Goterres kan cewa Iran tana bukatar ta ci gaba shirinta na makamashin nukliya ta zaman lafiya. Sannan a dauke mata takunkuman zaluncin da aka  daura mata.

Ya kuma kara da  cewa Iran tana daga cikin kasashen da suka sanya hannu a yarjeniyar NPT wacce ta bata samar  amfanin da makamacin nukliya ta zaman lafiya. Banda haka irana tana son ta shiga tattaunawa da kasashen Turai don warware matsalar shirin makamashin nukliya ta kasar ba tare da an harba harsashi go guda ba.

Ana bangare babban sakataren MDD ya yaba da tunanin tattaunawa ba kai tsaye ba , sannan ya taya kasar bakin ciki kan gobarara da ta tashi a tashar jiragen ruwa ta Ali Ra’ei a bandar Abbas.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments