Imam Sayyid Aliyul Khamani Ya Ce Dakarun Sa Kai Na Iran Wato Bashij Dashen Allah Ne

Jagoran juyin juya halinmusulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khamanae, ya bayyana cewa dakarun sa kai da ake kira Basij a nan Iran dashen

Jagoran juyin juya halinmusulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khamanae, ya bayyana cewa dakarun sa kai da ake kira Basij a nan Iran dashen All..ne don haka ne suka zama babban kariya ga kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Jagoran kuma babban kwamandan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa babu wata kasa a duniya wacce take da irin wannan dakaru masu sa kai kamar haka. Saboda ayyukansu na taimakawa raunana da kuma tafarkin fatarkin All..ne.

Jagoran ya bayyana cewa, tun shekaru 15 kafin nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran Imam Khomaini (q) yake tunnanin kafa Basij.

Jagoran ya yi wannan jawabin ne a lokacinda yake ganawa da dakarun sa kai na Basij, a safiyar yau litinin a Husainiyar Imam Khomaini (q) da ke gidansa.

Daga karshe dangane da shuwagabannin HKI kuma Jagoran ya bayyana cewa, dole ne a gufarnar da shuwagabnnin HKI a gaban kuliya saboda laifukan yakin da suka aikaya a kasar Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments