Imam Khaminae Ya Halarci Makokin Ashoora A Gidansa A Tehran

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya halarci zaman makokin da aka gudanar a hussainiyar Imam Khomaini (q) da cikin gidansa a

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya halarci zaman makokin da aka gudanar a hussainiyar Imam Khomaini (q) da cikin gidansa a nan birnin Tehran a daren Ashoorah a jiya Asabar da yamma.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hujjatul Islam Masaoud Ali wanda ya karanta makokin yana fadar cewa, kasar Iran zata dauki darasi daga Imam Hussain (a) na rashin mika kai da azzalumai.

Ya kuma bayyana yunkurin da Iraniyawa suke yi a halin yansu yana daga cikin gwagwarmayan duniya don fuskantar azzaluman duniya karkashin jagorancin HKI da Amurka.  

Ya kuma kara da cewa musulunci ne yake gaba da gaba da kafircin duniya a cikin yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka jagoranta kan JMI. Kuma wannan yunkirin da sauran masu gwagwarmaya a duniya zasu ci gaba da gwagwarmaya tare da jagorancin Imam Sayyid Aliyul Khaminae. Wannan dai shi ne bayyanar Jagoran a karon farko bayan yakin kwanaki 12.

Malamin ya kara da cewa, iraniyawa ba zasu mika kai ba har zuwa nasara kamar yadda muka koya daga Imam Hussain (a) hakan a ranar Ashoorah.

A lokacinda Mahmoud Karimi zai karanta makokin an ga Imam Khaminae (H) yana fadawa Karimi wani abu a kunnensa , inda daga baya Karimin ya bayyana cewa ya umurce shi y ace, kasata zaki wanzu a zuciyata da raina.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments