Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta nuna damuwa kan rahotannin baya-bayan nan na “kasha kashe, fyade, da sauran laifuka” da Rundunar Taimakon Gaggawa (RSF) ta aikata a yankin El-Fasher, na Sudan, tana gargadin cewa wadannan ayyukan na iya zama “laifukan yaki da cin zarafin bil’adama.”
“Irin wadannan ayyuka, idan aka tabbatar da su, na iya zama laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a karkashin yarjejeniyar Roma,” in ji sanarwar da Ofishin Mai Gabatar da Kara na ICC, ya fitar.
A cewar sanarwar, wadannan ayyukan sun lalata dukkan yankin Darfur tun daga watan Afrilun 2023,” ranar da aka fara yaki tsakanin sojojin Sudan da Rundunar Taimakon Gaggawa.
A cikin sanarwar, Ofishin Mai Gabatar da Kara ya tuna cewa, a karkashin kuduri na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1593 (2005), Kotun hukuntan manyan laifuka ta Duniya (ICC) tana da hurumin gurfanar da masu hannu a laifukan da aka aikata a rikicin da ke ci gaba da faruwa a Darfur.
Ta kuma bayyana cewa Ofishin yana binciken laifukan da aka aikata a Darfur tun bayan barkewar rikici a watan Afrilun 2023.
A ranar 26 ga watan Oktoba ne, Rundunar (RSF) ta kwace iko da garin El-Fasher tare da aikata kisan gilla ga fararen hula, a cewar kungiyoyin cikin gida da na kasa da kasa.
Rikicin da barke a ranar 15 ga Afrilu, 2023, tsakanin sojojin Sudan da RSF ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 20,000 tare da raba mutane sama da miliyan 15 da muhallansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da majiyoyin cikin gida.