Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya na neman shaidu kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
Matakin zai shafi irin ta’asar da aka aikata daga ranar 1 ga watan Janairun 2022 zuwa yau, bisa la’akari da tashe-tashen hankula da aka yi a makonnin baya-bayan nan musamman a birnin Goma – babban birnin lardin Kivu ta Arewa.
Kotun ta ICC ta ce an jikkata dubban mutane tare da kashe daruruwan mutane a birnin Goma da kewaye.
Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su har da fararen hula da dakarun wanzar da zaman lafiya, bayan shafe tsawon watanni ana gwabza fada tsakanin sojojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da kungiyar M23 da kawayenta.
Ofishin mai gabatar da kara ya yi kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, da shaidu, da kungiyoyin kasa da kasa, kungiyoyin farar hula, da su bayar da duk wata shaida da ke hannunsu, dangane da zargin laifukan da dukkan bangarorin suka aikata.
A nata bangaren, DRC tana shirin gabatar da kudiri ga kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya a wannan Juma’a a birnin Geneva na kasar Switzerland, na neman a gudanar da bincike kan abin da ta kira “gaggarumin take hakkin dan Adam” a birnin Goma.