Hizbullah Ta Yi Tir Da Harin HKI Akan Kasar  Syria

A wani bayani da kungiyar gwgawarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar a jiya Litinin ta yi Allawadai da hare-haren da sojojin HKI suke kai

A wani bayani da kungiyar gwgawarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar a jiya Litinin ta yi Allawadai da hare-haren da sojojin HKI suke kai wa a kasar Syria da kuma keta tsagaita wutar yaki a Lebanon,haka nan kuma cigaba da kai wa mutanen Gaza hare-hare.

Bayanin na kungiyar Hizbullah ya kuma bayyana cewa irin wadannan hare-hare na sojojin HKI yana cigaba da jefa al’ummar yankin a cikin hatsari na yau da kullum.

Har ila yau Hizbullah ta cigaba da cewa, yadda HKI take kara mamaye wasu yankuna a cikin yankin tuddan Gulan, da kuma kai hare-hare domin raunana sojojin Syria, suna a matsayin wuce gona da iri da keta hurumin kasar Syria gwamnati da kuma al’umma.

Kungiyar ta Hizbullah ta kuma ce, adaidai lokacin da take yin tir da wannan wuce gona da irin, tana kuma yin gargadi akan cigaba aikata shi, sannan kuma ta yi kira ga kasashen musulmi da kuma na larabawa da su dauki matakan da su ka dace akan wadannan irin laifuka, da kuma yin matsin lamba na siyasa da shari’a saboda kawo karshen hare-hare.

Har ila yau Hizbullah ta ce, babu yadda za a yi “Isra’ila” ta bai wa abinda take yi fuskar doka, sunan abinda take yi din mamaya.

A karshen bayanin kungiyar ta Hizbullah, ta bayyana cewa, tana tare da kasar Syria da al’ummarta, tare da jaddada wajabcin kare hadin kan kasar ta Syria da cigaba da zamanta dunkulalliyar kasa.

A daren jiya dai jiragen yakin HKI sun kai munanan hare-hare akan cibiyoyin sojan Syria, da rusa jirage masu saukar angulu na soja da tankokin yaki da kuma jiragen yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments