Husi: Kai Wa Kasar Katar Hari Gargadi Ne Ga Al’ummar Musulmi

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husy wanda ya gabatar da jawabi a yau Alhamis ya bayyana cewa: Makaman gwagwarmaya suna a matsayin

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husy wanda ya gabatar da jawabi a yau Alhamis ya bayyana cewa: Makaman gwagwarmaya suna a matsayin lamuni ne na hana abokan gaba yi wa al’umma kisan kiyashi da hare-haren wuce gona da iri.

Da yake Magana akan abinda yake faruwa akan doron ruwan “Red Sea” Sayyid Abdulmalik al-Husi ya ce; Duk wani yunkuri na bayar da kariya ga jiragen ruwan HKI, da kuma a cikin mashigan ruwa da suke a yankin, ba za su ci nasara ba.”

Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma ce; Dukkanin hare-haren da  su ka kai a makon da ya shude a ruwan “Red Sea” an kai shi ne akan jragen ruwan HKI kadai.

Har ila yau, ya kuma yi ishara da kisan kiyashin da HKI take ci gaba da yi wa al’umma Falasdinu a yankin Gaza, wanda lamari ne mai firgitarwa, kuma hakan ya tilasta wa duk wani ma’abocin lamiri a doron kasa daukar matsaya.

Bugu da kari, Sayyid Abdulmalik al-Husi ya ce, barazanar abokin gaba, ba ta tsaya akan Falasdinawa kadai ba, tana nufin dukkanin al’umma ne kadai,don haka bai kamata musulmi su yi sako-sako ba, ko su ci gaba da zama ‘yan kallon kisan da ake yi Falasdinawa.

Da ya koma Magana akan taron da aka yi a Doha ya bayyana cewa, jawabin bayan taro da aka yi, bai kai girman laifin da  ‘yan sahayoniyar su ka tafka ba. Haka nan kuma ya ce; Matakin mai rauni na taron Doha, zai karfafa ‘yan sahayoniya su ci gaba da wuce gona da iri.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted