Search
Close this search box.

Human Rights Watch : Hare-haren Isra’ila A Hodeidah Laifukan Yaki Ne

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta sanar da cewa hare-haren da Isra’ila ta kai a tashar jiragen ruwa ta Hodeidah a watan

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta sanar da cewa hare-haren da Isra’ila ta kai a tashar jiragen ruwa ta Hodeidah a watan da ya gabata kan fararen hula kan iya zama laifin yaki.

A ranar 20 ga watan Yuli, Isra’ila ta kai jerin hare-hare kan cibiyoyin mai da kuma wata cibiyar samar da wutar lantarki ta Hodeidah a kasar Yemen.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce an kashe akalla mutane shida tare da jikkata wasu akalla 80 a hare-haren da Isra’ila ta kai kan cibiyoyin masu mahimmanci na Yemen.

Hare-haren na Isra’ila data danganta da ramuwar gayya sun zo ne kwana guda bayan da kungiyar Ansarallah ta kaddamar da wani hari da jirgi mara matuki a Tel Aviv, inda ya kashe mutum guda.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta bayar da rahoton cewa, hare-haren da Isra’ila ta kai kan Hodeidah sun shafi tankunan mai sama da ashirin da manyan kugiya guda biyu a tashar ruwan, baya ga wata tashar samar da wutar lantarki a gundumar Al-Salif da ke Hodeida, sun shafi ababen bukatuwa na fararen hula da dukiyoyinsu.

Duk laifukan da aikata da gangan, ana daukarsu a matsayin laifukan yaki, a cewar kungiyar ta Human Rights Watch.

Rahoton na kungiyar ya kuma ce binciken da aka yi na hotunan tauraron dan adam ya nuna cewa tankunan man sun shafe akalla kwanaki uku suna ci, lamarin da ke kara haifar da matsalolin muhalli.

Tashar jiragen ruwa ta Hodeidah, wacce ke karkashin ikon dakarun kasar Yemen tun shekara ta 2021, tana taka muhimmiyar rawa wajen isar da abinci da sauran kayayyakin da ake bukata ga al’ummar kasar Yemen.

Kimanin kashi 70 cikin 100 na kayayyakin da ake shigowa da su Yemen na kasuwanci da kuma kashi 80 cikin 100 na kayan agajin jin kai suna wucewa ne ta wannan tashar jiragen ruwa.

Yemen dai ta ce ba makawa za ta mayar da martini kan harin na Isra’ila a tashar ruwan ta Hodeida.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments