Ofishin Watsa Labarai na Gaza ya ce sojojin Isra’ila suna ƙara ƙaimi wajen kisan kiyashi a arewacin Gaza, ciki har da sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia, tare da “luguden wuta da gangan” tun da suka soma kai hare-hare ta ƙasa a ranar 6 ga watan Oktoba.
“Sojojin mamaya sun hana masu akin ceto da tawagar masu bayar da ɗaukin gaggawa kwashe gawawwaki fiye da 75 na shahidai daga cikin shahidai 285 da suka kashe a hare-hare ta ƙasa,” in ji sanarwar da ofishin ya fitar.
Sojojin suna “aikata laifukan keta haƙƙin ɗan’adam da kuma yin kisa da gangan ta hanyar kai hare-hare da bama-bamai kan mutanen da suka raba da gidajensu da kuma cibiyoyin da suke samun mafaka, inda suke kashe fararen-hula da kuma kai hari kan taron mata da yara,” a cewar sanarwar.
Ofishin ya ƙara da cewa a yunƙurinta na ci gaba da yin kisan kiyashi, rundunar sojojin Isra’ila ta yi yunƙurin rusa dukkan fannin kiwon lafiya a arewacin yankin ta hanyar hana asibitoci gudanar da ayyukansu tare da kai hare-hare a cikinsu.
Ya yi gargaɗi game da shirin Isra’ila na mayar da “arewacin Gaza zuwa wani yanki da za a ruguza tare da kashe ɗaukacin mazaunansa, a wani ɓangare na korar Falasɗinawa daga yankin.”