Hukumar leken asiri ta gwamnatin Isra’ila (Shin Bet) ta amince da gazawarta wajen hana harin ba-zata da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, shugaban hukumar ta Shin Bet, Ronen Bar, ya amince da cewa, hukumar ta ” gaza a cikin aikinta” na dakile ayyukan Operation Al-Aqsa, tare da kutsawa manyan sansanonin Isra’ila bayan da sojoji da ‘yan sandan gwamnatin suka yi kaca-kaca da su.
Ya ce, da hukumar ta Shin Bet ta yi wani abu daban a cikin shekarun da suka gabata kafin harin da kuma a daren da aka kai harin… da an kaucewa hakan.
“A matsayina na shugaban hukumar, zan dauki wannan nauyi a wuyana har karshen rayuwata,” in ji shi.
Hukumar ta amince da gagarumin gibi a cikin tattara bayanan sirri da kuma dogaro da matakan kariya da ake da su, wanda ya haifar da rashin fahimtar kungiyar Hamas, tare da sauran kungiyoyin gwagwarmaya.
Wannan na zuwa ne kwanaki bayan wani “binciken cikin gida” ya nuna cewa, an gaza wajen dakile harin na Hamas.
Binciken da sojojin Isra’ila suka gudanar ya soki yadda gwamnatin kasar ke dogaro da bayanan sirri da kuma raina karfin Hamas, kura-kuran da suka haifar da mummunan sakamako ga gwamnatin Isra’ila.