Kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta yi Allah wadai da kalaman da fira ministan mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi game da kafa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya.
Sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar ‘yantar da Falasdinu Hussein Al-Sheikh ya bayyana cewa: Suna yin Allah wadai da matakin da mahukuntan yahudawan sahayoniyya suka dauka na kai cin mutunci da raina kimar masarautar Saudiyya da ‘yancinta, wanda suka yi kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya, kuma wannan furuci na Rashin tunani ya yi cin karo da dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar kasa da kasa.
Ya kara da cewa: Suna tabbatar da cewa: Kasar Falasdinu za ta kasance ce a kasar Falasdinu kawai, kuma suna jinjinawa matsayin masarautar Saudiyya da jagorancinta da al’ummarta, wadanda a kullum suke kira jaddada kare jaddada dokokin kasa da kasa da kuma kudurin samar da kasashe biyu na Falasdinawa da na yahudawan sahayoniyya a matsayin tushen samar da tsaro, kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin.