Dakarun kare juyin juya halin Iran sun yi gargadin kai hari ga duk wani jirgin ruwa na soja da ya yi yunkurin bi ta mashigin Hormuz.
Kalaman sun zo ne bayan rundunar sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya ta ce jiragen ruwan sojin Amurka biyu sun wuce ta mashigar, a karon farko tun bayan soma yakin.
Sai dai Tehran ta musanta wannan ikirari, tana mai cewa ita ce ke iko da mashigar ruwan.
Tun da fari, Washington ta ce dakarunta sun fara cire nakiyoyi daga mashigar, ikirarin da Tehran ta sake musantawa.
Wani jamiāin sojan Amurka ya ce kokarin na mayar da hankali ne kan samar da hanya mai tsaro ga jiragen kasuwanci.
Saidia Iran ta musanta ikirarin kwamandan babbar cibiyar ayyukan sojin Amurka (CENTCOM) na cewa jiragen ruwan Amurka sun ratsa ta mashigar Hormuz,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Fars, na Iran ya ambato mai magana da yawun shalkwatar rundunar tsaron Iran na bayyanawa.
“Amincewa da ratsawar duk wani jirgin ruwa na hannun dakarun jamhuriyar Musulunci ta Iran,” a cewar jami’in.