HKI:Har Yanzu Matatar Man Fetur Ta Haifa Ba Ta Koma Aiki Ba

 Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce, sai zuwa watan Oktoba ne za a iya kawo karshen lalacewar da matatar man fetur din Haifa ta yi sanadiyyar

 Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce, sai zuwa watan Oktoba ne za a iya kawo karshen lalacewar da matatar man fetur din Haifa ta yi sanadiyyar harin makami mai linzami na Iran.

Jaridar “Time Of Isra’il” ta bayyana cewa a tsawon yakin kwanaki 12, Iran ta yi wa Isra’ila mummunan harin mai ciwo da sai yanzu ne sannu a hankali zurfinsa yake bayyana.

A jiya Lahadi ne matatar man fetur ta Haifa ta sanar da cewa; Wani karamin sashe nata ne zai fara aiki, saboda hare-haren makamai masu linzami na Iran.

 Matatar man fetur din wacce ake kira da sunan : “BAZAN” ta ce sai zuwa wata Oktoba ne ake sa ran cewa za ta koma aiki baki daya.

A ranar 15 ga watan Yuni ne dai aikin matatar ya tsaya saboda hare-haren ramuwar gayya da Iran din ta kai, bayan da ‘yan sahayoniyar bisa cikakken goyon bayan Amurka su ka kawo wa Iran hari.

Ita dai wannan matatar man fetur din tana samarwa da HKI man fetur da ya kai kaso 59% da kuma Gas da ake amfani da shi a gidaje da ya kai kaso 52%.

A yayin harin, kamfani da yake tafiyar da matata ya sanar da halakar ‘yan sahayoniya 3.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted