HKI Tana Cigaba Da Hana Shigar Da Kayan Agaji Zuwa Yankin Gaza

Kwanaki 30 bayan tsagaita wutar yaki a Gaza, sojojin mamayar HKI suna cigaba da kai hare-hare a yankuna mabanbanta. Bugu da kari, sojojin na HKI

Kwanaki 30 bayan tsagaita wutar yaki a Gaza, sojojin mamayar HKI suna cigaba da kai hare-hare a yankuna mabanbanta.

Bugu da kari, sojojin na HKI suna cigaba da rushe gidajen Falasdinawa a cikin yankin yammacin kogin Jordan.

Minsitan kudi na HKI Byetrael Smotrach ya ce, a kowace shekara za su rushe gidaje a yammacin kogin Jordan fiye da wadanda Falasdinawa suke ginawa. Wannan dai shi ne lokacin farko da HKI ta dawo da siyasar rusau a yammacin kogin Jordan tun a 1967.

Wannan matakin na HKI yana zuwa ne a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Robio yake ziyara a Tel Aviv, kuma a lokacin da Amurkan ta bai wa HKI bama-baman MK-84 har guda 1,800.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments