HKI Tana Ci Gaba Da Keta Tsagaiwa Wutar Yaki A Lebanon

Tashar talabijin din ‘al-manar’ ta watsa rahoton da yake cewa; HKI tana ci gaba da keta tsagaita wutar yaki a kudancin Lebanon, ta hanyar kai

Tashar talabijin din ‘al-manar’ ta watsa rahoton da yake cewa; HKI tana ci gaba da keta tsagaita wutar yaki a kudancin Lebanon, ta hanyar kai hare-hare a cikin kauyuka mabanbanta da su ka hada Harsh- Yarun.

Dan rahoton na tashar talabijin din ta ‘al-manar’ daga kudancin Lebanon ya bayyana cewa; An ji karar fashewar masu karfi a garin Aitas-Sha’ab,bayan da HKI ta kai farmaki a unguwannin garin.”

Haka nan  kuma an ga sojojin na mamaya suna kai da komowa a tsakanin Yarun da Marun Ra’as da kuma a yankin Maisal-Jabal da kuma gefen garin Kafar-kala.”

 A gefe daya, sojojin yakin HKI sun rika yin shawagi a samaniyar kudancin Lebanon da hakan yake a matsayin keta wutar yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments