Ofishin da yake tafiyar da hukuma a Gaza, ya sanar da cewa daga tsaaita wutar yaki zuwa yanzu adadin motocin dake dauke da abinci da aka bari su ka shiga yankin ba su wuce 986 ba alhali yawansu ya kai 6600.
A bisa yarjejeniyar da aka kulla ta tsagaita wutar yaki, adadin motocin da ya kamata a bari su shiga yankin na Gaza, zuwa jiya Litinin 10/21/2025, shi ne 6,600.
Daga cikin kayan agajin da ake son shigar da su cikin Gaza da akwai tukwanen Gas na dafa abinci a cikin manyan motocin dakon kaya 14, da kuma wasu motocin 28 masu dauke da makamashin da gidajen Burodi, asibitoi za su yi aiki da su.
Yankin na Gaza dai yana fuskantar karancin makamashin da muhimman cibiyoyi suke da bukatuwa da su domin tafiyar da harkokin yau da kullum.
Yarjejeniyar tsagaita wutar yaki ta kunshi cewa a kowace rana za a bar manyan motoci 600 su shiga cikin yankin, sai dai adadin da suke shiga a yanzu ba su wuce 89 ba.
Wannan matakin da HKI take dauka na hana shigar da kayan agaji kamar yadda aka tsara, yana ci gaba da jefa mutanen na Gaza cikin yunwa.
Tun gabanin yakin Gaza dai, a kowace rana ta Allah, yawan motocin da suke shiga yankin dauke da kayan agaji suna kai wa 600. Sai da tsawon lokacin yakin ‘yan sahayoniya sun hana shigar da kayan abinci da magani, da hakan ya haddasa yunwa da mutuwar mutane da dama.