HKI Ta Tabbatar Da Halakar Sojojinta 2 A Yankin Rafa Na Zirin Gaza

Gwamnatin HKI ta bada sanarwan halakar sojojinta biyu da kuma jikatan wasu alokacinda suke bincike da kuma kokarin shiga wani rami na karkashin kasa a

Gwamnatin HKI ta bada sanarwan halakar sojojinta biyu da kuma jikatan wasu alokacinda suke bincike da kuma kokarin shiga wani rami na karkashin kasa a inda wani bom ya tashi ya kashe su ya kuma raunata wasu.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakafen yana labaran yahudawan na fadar haka a safiyar yau kuma wadanda aka rutsa da su sun hada da  Captain Noam Ravid, dan shekara 23 a duniya da kuma Staff Sergeant Yaly Seror, dan shekara 20 a duniya.

Labarin ya kara da cewa hatsarin ya faru ne a jiya asabar, sannan wasu sojoji biyu daga rundunar Yahalom sun ji rauni.

Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ne aka fara yakin tufanul Aksa, inda sojojin yahudawan tare da taimakon kasashen yamma suka fara kisan kiyashi ga Falasdinawa a yankin, wanda ya kaiga shahadar mutane 52,495 ya zuwa yanzu. Sannan wasu 118,366 suka ji rauni.

An dan tsaida yaki daga ranar 19 ga watan Jenerun wannan shekara har aka kai wata marhala sai HKI ta tsaida aiwatarda yarjeniyar. Sannan ta sake komawa yaki.

An kashe sojojin yahudawa fiye da 850 daga ciki har da sojojin kasa 414 a yankin na Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments