HKI Ta Tabbatar Da Cewa An Kashe Sojojinta Fiye Da Dubu Daya A Yakin Gaza

Ma’aikatar yakin HKI ta tabbatar da halakar sojojinta fiye da dubu guda a yakin tufanul aksa, wanda aka fara a yanar 7 ga watan Octoban

Ma’aikatar yakin HKI ta tabbatar da halakar sojojinta fiye da dubu guda a yakin tufanul aksa, wanda aka fara a yanar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023.

Tashar talabijin ta Al-Mayadden ta nakalto kafafen yada labaran HKI na fadar cewa, ma’akatar da ce an kashe sojoji 1152 tun bayan fara yakin tufanul Aksa tsakanin sojoji da wasu jami’an tsaron.

Labarin ya kara da cewa kashi 42% na wadanda suka halaka, wato 487 daga cikinsu basu kai shekara 21 a duniya ba. Sannan 141 daga cikinsu sun dara shekaru 40 a duniya.

Banda ya haka yakin ya samar da sauyi babba a cikin rayuwar yahudawan sahyoniyya. Sannan wadanda suka ji rauni kuma sun dara 18,500.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted