HKI Ta Sake Kashe Wasu ‘Yan Jaridar Falasdinawa 5

A wani hari da jiragen yakin HKI su ka kai kusa da asibitin “Al-Awdah” dake tsakiyar Gaza, sun kashe wasu  Karin ‘yan jarida 5. Kafafen

A wani hari da jiragen yakin HKI su ka kai kusa da asibitin “Al-Awdah” dake tsakiyar Gaza, sun kashe wasu  Karin ‘yan jarida 5.

Kafafen watsa labarun Falasdinawa sun ce ‘yan jaridar da su ka yi shahada suna aiki ne da gidajen talabijin na Al-Quds da Al-Youm, a daidai lokacin da suke shirya rahoto akan abinda yake faruwa a asibitin ‘al-awdah’.

Sojojin na HKI sun kai wa motar ‘yan  jaridar hari ne alhali tana dauka da tambarin dake nuni da cewa ta aikin jarida ce.

‘Yan jaridar da su ka yi shahada su ne; Fadi Hassouna, Ibrahim al-Sheikh Ali, Mohammed al-Ladah, Faisal Abu al-Qumsan da Ayman al-Jadi. 

Wannan dai ba shi ne karon farko da HKI take yi wa ‘yan jarida kisan gilla ba a tsawon lokacin yaki. Ya zuwa yanzu ta kashe fiye da ‘yan jarida 200 a cikin Gaza da kuma wasu yankuna na Falasdinu.

Adadin Falasdinawan  da su ka yi shahada a cikin watanni 14 sun kai 45,300,wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 107,800.

Da akwai wasu dubban Falasdinawan da suke a karkashin baraguzai da har yanzu ba a iya fito da su ba, saboda rashin kayan aiki da kuma cigaba da kai hare-haren da HKI take yi babu kakkautawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments